Assad yace ‘yantar da Aleppo ba nasara ce ga Syria kawai ba, nasara ce ga daukacin masu yaki da ta’addanci, musamman kasashen Rasha da Iran.
Kungiyar agaji ta Red Cross tace akalla ‘yan tawaye 4,000 ne suka fice daga gabashin Aleppo, yayinda ake ci gaba da kwashe fararen hula daga yankin.
Tun a shekara ta 2012 irnin Aleppo ya kasu gida biyu wato bangaren da sojojin gwanati ke iko da shi, da kuma yankin da ‘yan tawayen suka mamaye.
Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka masu sa ido 31 ke Aleppo domin ganewa idonsu yadda aikin kwashe fararen hular ke gudana.
Karbe gabashin Aleppo gagarumin koma baya ne ga yunkurin mayakan ‘yan tawaye Syria na kifar da gwamnatin kasar, wadanda suka kaddamar da fafutukarsu a shekara ta 2011.